Home Security Gwamna Dikko Radda Ya Kaddamar da Kwamitin Inganta Sasanci da janye makamai...

Gwamna Dikko Radda Ya Kaddamar da Kwamitin Inganta Sasanci da janye makamai ajahar Katsina

23
0
Daga Fatima Mukhtar Isah
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya kaddamar da Kwamitin Yaye Makamai, Sauke Mayaka da Mayar da Su Cikin Al’umma (DDR) tare da Kwamitin Zaman Lafiya da Tsaro domin ƙarfafa zaman lafiya da haɗin gwiwar tsaro a jihar.
An kaddamar da kwamitin ne a Muhammadu Buhari House da ke Katsina, a matsayin wani shiri na ƙasa ƙarƙashin Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro tare da haɗin gwiwar Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC) da shirin UK-SPRING.
Gwamna Radda ya bayyana cewa an zaɓi Jihar Katsina a matsayin ɗaya daga cikin jihohin gwaji saboda ƙoƙarin da take yi wajen amfani da hanyoyin haɗin kan al’umma da kuma dabarun lumana wajen magance matsalar tsaro. Ya ce kwamitin zai kula da yaye makamai, gyaran hali, mayar da masu tuba cikin al’umma, da ayyukan gina zaman lafiya.
Gwamnan ya buƙaci mambobin kwamitin su gudanar da aikinsu cikin ƙwazo, gaskiya da haɗin gwiwa da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dorewar zaman lafiya da tsaro a jihar.
Sakataren Gwamnatin Jihar kuma shugaban kwamitin, Barrista Abdullahi Garba Faskari, ya gode wa gwamnan bisa amincewar da ya nuna musu tare da alƙawarin gudanar da aikin cikin ƙwarewa domin cimma nasarar samar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da Mataimakin Gwamna, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, mambobin majalisar zartarwa ta jihar da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro.