Gidauniyar Lado Development Foundation tana sanar da Daliban Jami,ar Umaru Musa Yar’adua da suka halarci wurin tantacewa aranar 19/08/2025 domin abiya masu kudin makaranta, cewa Lado Development Foundation ta fiddo sunayan wa’anda zasu samu wannan tallafi na biyan kudin makaranta.
Awata Sanarwar Manema Labarai da Sakataran Lado Development Foundation Ghali Salisu Bakori ya bayar, Gidauniyar tayi kira ga Daliban shawara cewa su zama masu tausayi da kuma taimakon Uwayan su, kuma kar su koma su kara amsar wasu kudi awurin da sunan kudin biyan Makaranta. Domin kuwa Senator Yakubu Lado Dan-Marke ya dauke masu.

Wanann shine Rukuni na farko wato (Batch A). Ana kuma sanar da wadanda basu bayar da nasu takardun ba, ko kuma sun bada amma basu ga sunayan su ba, su kira ko tura sakon Watsapp zuwa ga wa’annan lambobin kamar haka:
Line 1: 08162538563
Line 2:07061604527
Line 3:0803 861 6869
ghalisalisubkr@gmail.com
Daliban da suka ga sunayensu a wanann Batch din da su fara duba portal dinsu daga ranar 21/08/2025
Daga karshe sanata yakubu Lado Dan Marke yayi kira da wadannan dalibai da su kasance masu kwazo da jajircewa yayin da suke daukar darussa a makarantun su.



