Ahmad Ibrahim.
Dan Takarar Kujerar Gwamnan Jihar Katsina akalkashin Jam’iyyar PDP Senator Yakubu Garba-Lado ya sha aliasing cewa zai yi kokarin magance matsalar tsaro ajahar ta Katsina acikin kwanaki Dari Daya idan ya hau Kujerar Gwamnan Jihar Katsina.
Senator Yakubu Lado ya fadi hakan ne alokacin da yake karbar daruruwan Yan Jam’iyyar APC kuma magoya bayan Kabir Murja political awareness group da suka fito fili domin baiyana komawar su Jam’iyyar PDP bayan sun fita daga Jam’iyyar APC ajahar Katsina.
Dan takardar Kujerar Gwamnan ha kokan akan yadda ake cigaba da rasa rayuka amma Gwamnati akowani mataki sai kauda ido takeyi kamar babu wata matsala ko kunci da mutane ke fuskanta.
Acewar “alokacin da ake kashe Mutane, Jamian Gwamnati sai bukukuwa sa sharholiya sukeyi, alhali kuwa Talakka sai kashe shi akeyi “
Awani kwarya kwaryan taro dai da aka gudanar awani dakin taron jama’a, Yan kungiyar ta Kabir Murja sun che basu samu kula ba a Jam’iyyar APC dan haka suka zabi komawa Jam’iyyar PDP domin goyon bayan Senator Yakubu Garba-Lado wanda ke takarar gwamnan jahar Katsina azaben 2027 mai zuwa.

Shugabannin Kungiyar daga Kananan hukumomi 34 sun wakilci Yan kungiyar ne domin baiyana komawar su Jam’iyyar PDP da manufar bada goyon bayan su ga Dan Takarar Gwamna na PDP





