Daga Muhammad Awwal.
Rasha ta ce ba za ta iya karɓar shawarwarin Amurka ba ayunkurin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine ba, kamar yadda matakan suke ahalin yanzu, saboda achewar Rasha makakan ba su magance matsalolin da suka haddasa rikicin ba.
Alamu na nuna cewa tattaunawar tsagaita wuta ta tsaya chak, a inda Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar Rasha, Sergei Ryabkov, ya bayyana cewa har yanzu babu wata fahimta tsakanin Rasha da Amurka.
Ya kara da cewa shawarwarin da Shugaba Vladimir Putin ya gabatar fiye da makonni biyu da suka gabata akan Amurka ta yi gyra akan shawarwarin, amma Amurka batayi gyaran ba.



