Safiya Hambali Gafai.
Gwamna Dukko Radda na jahar Katsina ya nuna farin cikinsa da yadda Katsina ta bunkasa tun lokacin da aka kirkiro jahar Katsina Ya jaddada cewa jihar ta fuskanci kalubale daban-daban.
Gwamnan ya jinjina wa daukacin Al’ummar jihar, wajen jajircewa da nuna juriya akan cigaban jihar, da kuma shugabannin da suka gabata wadanda gudunmawar su ta gina tubalin da jahar ke bisa shi a yau. Ya kuma bayyana cewa hadin gwiwa tsakanin gwamnati, masarautun galgajiya, da talakawa shi ne silar ci gaban da ake gani a jihar.
Gwamnan Radda ya sake nanata cewa, samar da tsaro shine babban abunda Gwamnantin sa ta sanya a gaba. Inda ya Yabawa Hukumomin tsaro kan kokarin da sukeyi na kare rayuka da dukiyoyin Al’ummar jahar Katsina.
Haka kuma ya bayyana cewa shirye- shiryen samar da aiyukan yi da koyar da Sana’o’i suna taimakawa matuka wajen rage radadin tsaro da kawar da matsalolin ta’addanci.
Gwamna Dikko Radda ya sake jaddada kudurin Gwamnantin sa na sauya fasalin jahar ta hanyar zuba hannun jari a fannonin ilimi, kiwon lafiya da kuma fannin noma.
Daga karshe, Malam Dikko Umaru Radda ya yi kira ga daukacin ‘ya ‘yan jihar Katsina da ke gida da waje da su hada karfi da karfe, su goyi bayan kudurorin gyara na gwamnati don ciyar da jihar gaba. Ya roki al’umma da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda da kuma taya jihar da addu’o’in samun dorewar zaman lafiya da wadata.



