Safiya Hambali Gafai.
samukarin Mutane masu amfani da tsarin inshorar kula da kiyi lafiya ajahar Katsina.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana hakan ne yayin da ya ƙaddamar da rajistar sabbin masu amfana 184,105 a shirin Basic Health Care Provision Fund (BHCPF) a faɗin mazabu 361 na jihar.
Ya ce wannan gagarumin ci gaba ya samo asali ne daga manufofi da tsare-tsaren gwamnatinsa, na faɗaɗa damar samun ingantacciyar kulawar kiwon lafiya, da kuma kare al’umma daga matsala ta rashin kuɗaɗen jinya.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa masu amfana da tsarin inshorar lafiya a Jihar Katsina sun ƙaru, daga mutane dubu dari uku da hamsin da biyar (355,000) a shekarar 2023 zuwa mutane dubu dari biyar da tamanin da uku da dari hudu da sittin (583,460) a shekarar 2026, wanda ke nuna ƙarin kusan kashi 64 cikin 100 cikin shekaru uku.
Gwamna Radda ya bayyana cewa hukumar Katsina State Contributory Healthcare Management Agency (KTSCHMA) ta samu lambar yabo ta Mafi Kyawun Hukumar Inshorar Lafiya ta Jiha a ƙasa a shekarun 2024 da 2025. Ya ƙara da cewa jihohi bakwai sun kai ziyara Katsina domin nazarin sabbin dabarun da jihar ke amfani da su wajen gudanar da inshorar lafiya.
Ya kuma bayyana wasu daga cikin manyan ayyukan da gwamnati ta aiwatar, ciki har da farfaɗo da Cibiyoyin Kula da Lafiya na Farko a kowace mazaba, kafa cibiyoyin binciken cututtuka, maganin cutar daji da wankin jini, da kuma inganta wasu cibiyoyin lafiya zuwa General Hospitals.
Gwamnan ya kuma sanar da cewa rajista a tsarin inshorar lafiya za ta zama wajibi ga masu cin gajiyar shirye-shiryen ƙarfafa tattalin arzikin gwamnatin jihar, domin kare su daga amfani da jarinsu wajen biyan kuɗaɗen jinya.
Ya ce gwamnati ta kuma shigar da ’yan fansho, Jami’an Hisbah, Community Watch Corps, da masu buƙata ta musamman cikin tsarin inshorar lafiya kyauta.
Gwamna Radda ya ƙara da cewa jihar ta biya Naira miliyan 243 a matsayin kuɗin haɗin gwiwa na BHCPF Matching Grant, tare da ƙarfafa tsarin samar da magunguna da amfani da fasahar zamani wajen bibiyar masu rajista da ayyukan kiwon lafiya.
A nasa jawabin, Kwamishinan Lafiya, Hon. Musa Adamu Funtua, ya bayyana ƙarin masu amfana da inshorar lafiya a matsayin wata babbar nasara, yana mai cewa hakan zai faɗaɗa damar samun kulawar lafiya tare da rage nauyin kuɗaɗen jinya ga al’umma.
Shi kuwa Daraktan-Janar na KTSCHMA, Hon. Muhammad Safana, ya yaba wa Gwamna Radda bisa goyon bayan da yake bai wa hukumar, yana mai tabbatar da cewa za ta ci gaba da faɗaɗa inshorar lafiya da inganta ayyukanta.
Hakanan shima shugaban Babban Asibitin Katsina ya bayyana cewa ƙarin masu inshorar lafiya zai ƙarfafa mutane wajen neman magani da wuri tare da samar wa asibitoci ingantaccen tsarin samun kuɗaɗen gudanar da ayyuka.
A nasa ɓangaren, Shugaban Hukumar Gudanarwa na hukumar KTSCHMA, Hon. Isah Kaita Damale, ya jaddada muhimmancin kyakkyawan shugabanci, gaskiya da rikon amana wajen tabbatar da dorewar nasarorin da aka samu.
Gwamna Radda ya kuma bayyana cewa Jihar Katsina ta fara shirin kafa Tsarin Samar da Kuɗaɗen Kiwon Lafiya, domin kare nasarorin da aka samu da tabbatar da dorewar tsarin inshorar lafiya ga al’ummomi.
Shirin ya samu halartar kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, Rt. Hon Nasir Yahya Daura, Sakataren Gwamnatin Katsina, Barr. Abdullahi Garba Faskari, Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir, Shugaban Hukumar yaki da cutar sida, Dr. Bala Nuhu Kankia da sauran masu ruwa da tsaki.



