Home Agriculture ZA’AFARA HADA TARAKTA AJAHAR KATSINA.

ZA’AFARA HADA TARAKTA AJAHAR KATSINA.

161
0

AISHA MUKTHAR.

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya kai ziyarar duba aikin hada tarakta na zamani na Tashar Bala da ake ginawa.

Tashar dai za ta rika ajiye taraktocin da aka shigo da su daga kasar Sin ba da dadewa ba, kuma za ta yi aiki a matsayin cibiyar horar da matasan da aka zabo daga dukkan kananan hukumomin aikin manyan injuna.

Gwamnan ya gamsu da irin aikin da ake yi a wurin tare da yin musabaha da ma’aikatan. Ya samu rakiyar wasu jami’an gwamnati da suka hada da Dr. Faisal Kaita, kwamishinan filaye da tsare-tsare; Hon. Abdullahi Ahmed Turaji, Babban Sakataren Gwamnan Jihar; Alhaji Kabir Bature (Sarkin Alhazai), Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai; da Alhaji Mansur Ahmed, Sarkin Arewan Daura.