IRAN BA ZA TA TAƁA RUSHEWA BA!!!
Ta yaya aka kai mana hari? Wannan shi ne karo na farko a tarihin duniya da hukumomin leƙen asiri guda goma sha biyu daga manyan ƙasashen duniya suka haɗu a lokaci guda domin aiwatar da farmaki na bai ɗaya a wuri ɗaya a doron ƙasa.
Wannan yaƙi ya ɗauki tsawon kwanaki goma sha biyu, kuma ba za ku iya hasashen irin girman yaƙin bayan fage (leƙen asiri da bayanan sirri) da matasanmu suka dakile ba.
Sun shirya manyan ayyukan ɓoye guda biyar da za a aiwatar cikin kwanaki da darare biyar:
Aiki na Farko: Kashe Jagora Rahabar.
Aiki na Biyu: Kashe manyan jami’an gwamnati 250 — wato kwakwalwa, idanu, kunnuwa, harshe, hannaye da zuciyar tsarin mulki; ma’ana gurgunta gwamnati gaba ɗaya.
Aiki na Uku: Kai hare-hare kan wurare masu matuƙar muhimmanci 300 a faɗin ƙasar: tashoshin wutar lantarki, madatsun ruwa, duk abin da ya shafi ruwa, wuta, iskar gas, sadarwa, man fetur da dizal — wato rufe ƙasar gaba ɗaya.
Aiki na Hudu: Hura rikicin jama’a mai faɗi — tarzoma da kisan jama’a a tituna tare da shigar ’yan bindigar Komala cikin birane.
Aiki na Biyar: Harin ’yan ISIS da ke kusa da Baku a Azerbaijan, tare da iyalansu, ta iyakokin Khoda Afarin, Bileh Savar da Pars Abad zuwa Ardabil da Tabriz domin kashe al’ummar Azerbaijan.
Bugu da ƙari, an shirya ’yan ISIS guda 5,000 da ke Afghanistan kusa da Khorasan su kai hari Mashhad domin kashe maziyatan Imam Reza (A.S).
Haka kuma, an shirya kashe-kashe ta hannun mabiya Rigi a kudu maso gabashin ƙasar, da kuma ’yan bindigar “Arab Creation” a Khuzestan.
Makonni biyu kafin yaƙin, an tara dukkan ƙungiyoyin adawa da gwamnati a birnin Brussels, inda aka umurce su da cewa:
“Ku yi duk mai yiwuwa domin kifar da tsarin mulki.”
Sun amince su kai babban hari a Tehran, suna da tabbacin cewa tsarin zai rushe.
TO, ME YA FARU?
Na Farko: Yaƙin tsaro da leƙen asirinsu ya sha mummunan kaye, duk shirye-shiryensu sun lalace.
Na Biyu: Matasanmu a fannin yanar gizo (cyber) sun kafa tarihi. Idan kuka ji kalmar “hacker”, ku sani cewa sun yi ƙoƙarin kutsawa cikin tsarin kariyar sararin samaniyarmu. Sun ce:
“Cikin awanni 120, dole ne a lalata dukkan tsarin Iran domin kai hare-hare a jere.”
Sun shiga tsarin a daren Juma’a da ƙarfe 2:30 na dare.
Daga 3:05 zuwa 3:20, sun kai hari kan wasu kwamandoji.
Sai dai kutse ɗin da aka shirya ya ɗauki awanni 120, matasanmu suka katse shi da ƙarfe 1:30 na rana washegari.
Sun yi kutse a Babban Banki, matasanmu suka katse shi suka dawo da shi.
Sun yi kutse a tsarin rarraba man fetur, matasanmu suka gyara shi.
Sun yi kutse a tsarin zirga-zirgar jiragen ruwa, matasanmu suka dawo da ikonsu akai.
Sun yi kutse a tsarin rarraba dizal, matasanmu suka ’yantar da shi.
A takaice: an ƙaddamar da yaƙin yanar gizo na duniya a kanmu, amma sun sha kaye kasa warwas.
Amma a ganina, abu mafi muhimmanci a wannan yaƙin na kwanaki goma sha biyu wanda ya ba duniya mamaki ya kuma rikitar da manyan janarori, shi ne jagoranci kai tsaye na Babban Kwamandan Rundunonin Soji (Rahabar) Allah ya kara kare mana Jagora.
Ya umarci kwamandoji da cewa:
“Admiral Tangsiri, Rundunar Ruwa ta IRGC ba za ta shiga ba, babu jiragen ruwa, babu jiragen ƙasa, babu makamai masu linzami.”
“Ga Rundunar Ruwa ta Soja: kada ku shiga.”
“Ga Rundunar Sama: kada ku shiga.”
Sannan ya ce:
“Dole ne Rundunar Basij ta shiga.”
A rana ta uku, ya ba da umarnin su shiga filin daga. Suka rufe dukkan hanyoyin shiga birane, ƙauyuka da yankuna, abin da ya ba maƙiya mamaki yayin da suka tarar duk hanyoyi sun toshe.
An kama jiragen yaki marasa matuƙa (drones) da dama a bayan manyan motoci!
An gano ƙananan drones da aka ɓoye a bayan motocin ɗaukar kaya!
Kwamandan ya tsara rundunoninsa da cikakkiyar daidaito.
Da yammacin Juma’a, an naɗa mataimaka da kwamandoji a muƙamansu.
A wannan Juma’ar, Kwamandan ya umarci Sayyid Majid Mousavi da cewa:
“Ku harba makamai masu linzami 120.”
An tambaye shi:
“Ina za mu kai hari?”
Sai Kwamandan ya ce:
“Ku kai hari kan kariyar sararin samaniyar maƙiya.”
Tsawon dare uku, an kai hari kan kariyarsu.
A dare na huɗu, an kai hari wurare 40. 39 sun yi nasarar fadawa inda ake bukata ba tare da wata matsala ba, sun bugu sosai.
A dare na biyar, an harba makamai masu linzami Fattah-1 guda 68, dukkansu sun kai inda aka nufa.
Yaushe Netanyahu ya kira Amurka da Turai yana ihu:
“Ku ceci mu! Muna son tsagaita wuta!”?
A daren biyar, lokacin da ya ga wutar “Fattah”, ya ji karar ta, kuma kariyarsu ta rushe.
A darare na biyar, shida, bakwai da takwas, harbin Fattah ya ci gaba.
A darare na takwas, tara, goma da goma sha ɗaya, Kwamandan ya ba da izinin harba makaman Khaibar.
A daren goma sha biyu aka kai harin ƙarshe.
Kwamandan ya ce:
“Ku kai hari guda ɗaya da sunan Khorramshahr.”
Har yau duniya na cikin mamaki game da makamin “Khorramshahr” da aka harba.
Kuma har zuwa yau, Kwamandan bai ba da izinin amfani da makamin “Rastakhiz” ba.
Duk da wannan tsari da aiwatarwa da manyan shaidanu na duniya suka yi, duk da haka sun gaza.
Shin wannan ba mu’ujiza ta Allah ba ce wajen karewa da ci gaban wannan ƙasa?
Da fatan za a yaɗa wannan saƙo sosai domin ya kai ga kowa don wayar da kai.



