Muhammad Yahaya.
sanarwa da kwamitin yakin neman zaben Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya fitar ranar Alhamis, ya ce shugaban kasar zai je jahohi 12 ne daga cikin jahohin Nijeriya 36 da Abuja domin yakin neman zabe.
Da ma dai Shugaba Tinubu ya bayyana cewa zai zauna a Abuja domin gudanar da ayyukan ci-gaban kasa saboda “Nijeriya tana bukatar karin kulawa a yanzu fiye da a kowane lokaci a baya.”
Sai dai ya ce “zan ware lokaci da zan yi magana kai-tsaye da ‘yan Nijeriya” yayin da kwamitin yakin neman zabensa zai jagoranci kamfe a jahohin da kananan hukumomi.



