Hambali Gafai.
Gwamnatin jihar katsina ta karyata zarge-zargen da ake cewa, ta dauki nauyin aikin Hajj ga shugabbanni yan bindiga ko wasu dake da hannu a ayyukan ta’addanci.
A cikin wata sanarwa da aka fitar, ta bayyana cewa kalaman da Bishir kurfi yayi a wani shire na kaitsaye na gidan talebijin na Trust TV basu da tushe balle makama.
Gwamnantin jihar ta bayyana zargin a matsayin karya tsagwaronta da kuma yaudara ga jama’a, an kir kireshi ne domin kawo cikas ga kokarin da Gwamnanti da Hukumomin tsaro keyi na magance matsalolin tsaro a fadin jihar.
Sanarwar ta nuna damuwar Gwamnanti kan yadda ake yada irin wadannan zarge- zargen, a dai dai lokacin da Hukumomin tsaro tare, da goyon bayan Gwamnanti jihar, ke samun gaggarumar nasara a yaki da yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a tsakanin al’umma.
Haka kuma, Gwamnantin jihar katsina tana zargin cewa wasu tsirarrun mutane da kungiyoyi, na kokarin siyasantar da harkokin tsaro domin cimma manufofinsu na siyasa, da kuma na radin kandi. Ta bayyana cewa wasu daga cikin wadannan mutane basu gamsu da yadda Gwamnanti taki amincewa da wasu tsare-tsaren su da take ganin zasu kwashe arziki kasa da ayyukan cigaba da suka shafi al’umma jihar katsina.
Bisa ga haka, ta kalubalanci masu wannan zargin dasu kawo hujjoji sahihai kuma ingantattu, domin tabbatar da gaskiyarsu. Ta kuma yi gargadin cewa,idan suka kasa kawowa, Gwamnanti zatayi amfani da dukkan hanyoyin da doka ta tana,domin kare martabarta tare da hukunta masu yada labaran karya da Batanci.
Kazalika, tayi kira ga al’ummar jihar katsina da sauran yan Nijeriya, dasu bama Hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki goyon baya wajen maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma ingantaccen tsaro a jihar katsina .
Gwamnanti a shirye take wajen bada dukkan goyon baya wajen cigaba da inganta tsaro da zaman lafiya mai lumana ga dukkan mazauna.



