Home Opinion Yadda Iraniyawa ke sadaukar da kan su domin kare Musulunci.

Yadda Iraniyawa ke sadaukar da kan su domin kare Musulunci.

139
0
Iran ta ba wa ƴaƴanta ruhi. Su kuma sai suka ba ta rayuwa, da ƴanci da kuma izza. Jamhuriyar Musulunci kenan.
Tsayuwar Iran wajen kare mutuncinta a yau sakamako ne na tsayuwar wasu ƴaƴanta. Su suka raya ta, su suka mayar da ita abin da muke gani.
Wannan shi ne Hassan Moghadam. Janaral ɗin sojan kare juyin juya halin kuma masanin kimiyya. Haifaffen birnin Tehran, ana masa laƙabi da Uban Tsuntsayen Farisa.
General Moghadam ne ya shimfiɗa asasin dukkanin fitinannun tsuntsayen da muke gani suna tasowa daga Iran zuwa gwalalon Aflaɗinu cikin ƴan daƙiƙu.
Ya yi mu’amala da malaman kimiyyar Russia, Koriya, da Suriya. Ya haɗiye fasahar waɗannan ƙasashe. Ya kawo gida Iran, sannan ya ɗora bisa ayyukansu dukka.
Tarihin Iran yana cike da sunayen mazaje waɗanda suka ba da komai nasu don ganin Jamhuriyar Musulunci ta tsaya da ƙafafunta.
Mafi shaharar shi ne General Ƙasimu Sulaiman. Zaman gida da jin daɗin rayuwa gabaɗaya ya sadaukar, ya zabi rayuwa a filin daga. A wajen Iran.
Yau yana Iraƙi, gobe yana Luban, jibi kuma Suriya. A ƙoƙarin tsarewa da tare gida. Dirkar Farisa kenan.
Maƙiya sun iya afkar da yaƙi da ta’addanci a kan Iran da al’ummar Iraniyawa ne a bayan shahadarsa.
Akwai likitan ilmi Dr Mostafa Chamran. Ɗaya daga cikin mafi kyan kwanyar Iran na dukkan zamani. First class, Distinction, Pioneer researcher. Simply the best!
Jami’o’in Amurka sun yi masa tayin gida, mota, da kulawa ta musamman da shi da iyalansa idan ya karɓi ya yi musu aiki. Amma Dr Chamran ya ƙiya. Ya ce gida zai koma.
A jami’o’in gargajiya na Iran ya yi ta ƙoƙarin zubawa, cikin ƙwaƙwalen Iraniyawa, dukkan ilmomin da ya kwaso daga Yammacin duniya.
A shekarar 1980 Amurka ta ingiza shugaban Iraƙi na wancan lokacin Saddam Hussein, ta ba shi makamai da kariyar siyasa ya faɗa wa Iran da yaƙi. A wannan lokacin Dr Chamran ne Ministan Tsaro na Jamhuriyar Musulunci.
A wannan halin Dr Chamran ya sanya khaaki ya jagoranci runduna don fuskantar abokan gaba. Saddam ya fesawa ƙauyen da Gen. Chamran yake ba wa kariya guba. A nan Dr ya yi shahada.
Prof. Seyyed Mohammad Marandi ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa yunɓum da aka ƙwaba, aka halicci Iraniyawa daban ne. Wallahi na yarda.
4. Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci, Ayatollah Mojtaba Khamenei wanda aka tabbatar jiya, sojan sa-kai ne lokacin yaƙin Saddam. A lokacin kuma mahaifinsa Shahid Ayatollah Ali Khamenei ne shugaban ƙasa.
5. Shugaban ƙasar Iran na yanzu, Dr Masoud Pezeshkian, a wancan lokacin yaƙin ɗalibin likitanci ne. A filin daga ya yi practical clinicals ɗinsa.
6. Shi kansa Seyyed Marandin — wanda ya kasance fuskar Iran a kafafen yaɗa labarai na Amurka da Turai da social media — haifaffen Amurka ne. A holder of the American passport.
Amma wannan alfarmar ta duniya ya bari, ya zaɓi ya tsaya ga Iran ɗinsa. Kuma shi ɗin ma sojan sa-kai ne. Ya tsira ne ma daga gubar da Saddam ya fesa masa.
Al’amarin Iran sai Iraniyawa. Harka ce ta cikakken imani, tsananin kishi da zallan sallamawa.