Daga Fatima Mukhtar Isah
Fitaccen malamin addinin Musulunci da ke garin Zariya a Jihar Kaduna, Sheikh Usman Idris Kusfa, wanda aka fi sani da Rigi-Rigi, ya rasu yana da shekaru 57 a duniya.
An tabbatar da rasuwar malamin a ranar Litinin da wani babban almajirinsa, Nasiruddeen Umar, wanda aka fi sani da Baharu, ya sanar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Zariya.
A cewar majiyar, Sheikh Kusfa ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Litinin a wani asibiti mai zaman kansa da ke Kaduna, bayan fama da doguwar jinya.
Sheikh Rigi-Rigi ya shahara sosai wajen wa’azi da koyarwar Musulunci, lamarin da ya sa ya samu mabiya da dama a cikin Jihar Kaduna da kewayen ta.
A ‘yan shekarun nan, ya kara shahara a kafafen sada zumunta, inda darussansa ke samun dubban masu kallo.
Marigayi malamin ya kasance abin girmamawa saboda tsayayyun ra’ayoyinsa kan fikihun Musulunci da koyarwar tarbiyya, hakan yasa rasuwarsa ta jawo alhini da ta’aziyya daga malamai, mabiya da al’ummar Arewa baki ɗaya.
Ya rasu ya bar mata, ‘ya’ya da jikoki. Rahotanni daga iyalan sa, sun an gudanar da sallar jana’izarsa a ranar Litinin dinnan a yankin Kusfa da ke garin Zariya ns Jihar Kaduna.



