Kungiyar Lawyoyi ta Najeriya wato NBA atakaiche, ta baiyana kafa dokar ta baci da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi ajahar Rivers amatsayin wani karan tsaye ga dokar kasar wato Constitution da kuma tsarin Dimokradiyya a Najeriya.
Wannan matsayin yana acikin wata sanarwar da Shugaban Kungiyar Lawyoyi ta Najeriya NBA Mazu Afam Osigwe SAN ya sanya ma hannu adaran Talata 19 ga watan Maris 2025 jim kadan bayan da shugaban Najeriya ya aiyana dokar tabaci ajahar ta Rivers.
Kungiyar Lawyoyin ta che duk da sashe na 305 na kundin tsarin mulkin Najeriya ta ba shugaban kasa damar kafa dokar ta baci, amma sashen ya aiyana wasu tsauraran matakan da dole sai an bi su kafin akafa dokar domin kar ayi ma Dimokradiyya ko yancin wani karan tsaye.
Kungiyar ta Lawyoyi ta che tsarin mulkin Najeriya na 1999 bai ba shugaban kasa ikon cire duk wani zaɓenɓen Gwamna, kk Mataimakin Gwamna, Ko Danmajalisa ba. Amma sashe na 188 ya baiyana karara yadda za’a cire Gwamna ko Mataimakin shi. Kuma akwai tanadi na tsarin da kuma dokar zabe ta kasa da akebi domin cire Danmajalisa ko rushe majalisar dokoki. Amma babu ko daya da akabi dokin aiyana dokar tabaci ajahar Rivers.
Kungiyar NBA ta che dakatar da Gwamnan jahar Rivers, da Mataimakiyar shi, da Yan majalisar dokoki ta saba ma kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma rikicin siyasar na jahar Rivers bai kai matsayin da za’a aiyana dokar tabaci ba.
Kungiyar Lawyoyi ta Najeriya ta kawo misalin yadda sashe na 305 karamin sahe na (3) acikin baka ya kawo irin dalilan da ake la’akari da su kafin a kafa dokar ta baci. Daga ciki akwai
1. Yaki ko kuma wata Barazanar cikin gida.
2. Ko wani far gaba,ko baiyanannan al’amari da zai iya kaiwa ga mamayar kasa.
3. Ko wani Rikicin da baza’a iya amfani sa shi ba ta hanyar lumana.
4. Ko wata Barazana akan dayancin Najeriya.
5. Ko aukuwar wata annoba awata jaha ko sashen ta.
6. Ko kuma wata Barazanar da zata ita shafar Najeriya amatsayin Taraiyya.
Kungiyar ta NBA tayi soki matakin na shugaban Najeriya da kakkausar murya, kuma tayi kira ga Majalisar dokokin Najeriya akan kar ta aminche da dokar tabaci da akan kafa ajahar Rivers.



