Aisha Muhammad Mukthar.
Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya bi sahun sauran Gwamnonin da suka taimakawa uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu wajen raba tallafin kayan abinci ga mambobin kungiyar Kiristocin Arewacin Najeriya wato CNNPF.
Taron wanda ya gudana a Filin taro na Murtala Muhammed Square dake agarin Kaduna, ya samu halartar uwargidan mataimakin shugaban kasa Nana Kashim Shettima, matan gwamnonin jahohi da kuma tsohon gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari da kuma Alhaji Ibrahim Masari babban mataimaki na musamman ga Shugaban Kasa Kan Siyasa Da Sauran Al’amura.

Wannan karamcin anyi ne don tallafawa iyalai marasa karfi a lokacin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara masu zuwa, tare da nuna jajircewarta akan taimakawa yankunan da ba su da galihu.



